Acts 24

Shariʼa a Gaban Felis

1Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna. 2Saʼad da aka shigo da Bulus, sai Tertullus ya shiga kai ƙararsa a gaban Felis yana cewa: “Mun daɗe muna zaman lafiya a ƙarƙashinka, hangen nesanka kuma ya kawo gyare-gyare a wannan ƙasa. 3Koʼina da kuma a kowace hanya, ya mafifici Felis, mun amince da wannan da godiya marar iyaka. 4Amma don kada in ƙara gajiyar da kai, ina roƙonka ka yi haƙuri ka saurari ɗan taƙaitaccen jawabinmu.

5“Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana ta da na zaune tsaye a tsakanin Yahudawa koʼina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa 6har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi. 7
This verse is empty in this translation.
8Ta wurin
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da shi mun kuma so mu hukunta shi bisa ga dokarmu. 7 Amma shugaban ƙungiyar soja, Lisiyas, ya zo ƙarfi da yaji ya ƙwace shi daga hannuwanmu 8 ya kuma umarci masu zarginsa su zo gabanka. Ta wurin
bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”

9Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.

10Da gwamna ya yi masa alama ya yi magana, sai Bulus ya amsa, ya ce: “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina. 11Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba. 12Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina ta da hankalin jamaʼa a majamiʼu ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba. 13Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba. 14Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa, 15ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka. 16Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.

17“Bayan ʼyan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka. 18Ni tsarkake ne saʼad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina ta da hankali ba. 19Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina. 20Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi saʼad da na tsaya a gaban Majalisa—  21sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa: ‘A game da tashin matattu ake mini shariʼa a gabanku yau.’ ”

22Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shariʼa.” 23Ya yi wa jarumin umarni yǎ tsare Bulus amma yǎ ba shi ʼyanci yǎ kuma bar abokansa su lura da bukatunsa.

24Bayan ʼyan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. 25Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.” 26A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yǎ yi magana da shi.

27Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so ya biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.

Copyright information for HauSRK